Yadda kisan wata mace da 'ya'yanta shida a Kanon Najeriya ya haifar da firgici
HomeMu Zagaya Duniya › Episode

Yadda kisan wata mace da 'ya'yanta shida a Kanon Najeriya ya haifar da firgici

18:56 Jan 24, 2026
About this episode
Shirin na wanan makon zai soma ne daga Tarayya Nigeria inda kisan Fatima Abubakar ƴar shekara 35 a duniya da ƴaƴanta 6 da wasu marasa imani su kayi ranar 17 ga wanan watan a Unguwar Ɗorayi Chiranchi da ke Kano ya girgiza duniya . Wanan kisan  da ke zaman mafi muni da aka gani a yan taakanin nan ya sake fito da  girman matsalar dabanci da ke addabar wanan  jihar mafi yawan al’umma a arewcin Najeriya. Zargin sace Christoci sama da 100  yayin da suke tsaka da ibada  ranar 18  ga wanan watan a karamar Kajuru na Jihar Kaduna a arewacin Najeriya ya tayar kura matuka a makon da mu kayi bankwana kamar yadda Joseph Bawa guda daga cikin yan uwan mutanen da akayi garkuwa dasu ya tabbatar wa RFI. Waɗannan da ma wasu na ƙunshe a cikin shirin na Mu Zagaya Duniya. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Select an episode
0:00 0:00