About this episode
A daren Laraba zuwa wayewar ranar Alhamis, filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai da ke jamhuriyar Nijar ya fuskanci wani hari na ɗan lokaci daga wasu mayaka na ƙungiyar IS. Gwamnatin sojin Nijar, tare da taimakon sojojin Rasha,ta murkushe maharan. A yanzu haka,jiragen sama sun ci gaba da zirga-zirga, a cewar hukumar da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama na ƙasar.