Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya
HomeIlimi Hasken Rayuwa › Episode

Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya

10:00 Feb 17, 2026
About this episode
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar. Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa wasu daga cikin jami'an hukumomin da ke kula da shirya jarabawa a matakai daban-daban na taimakawa wannan mummunar ɗabi'a ta satar jarabawa ta hanyar fallasa amsoshin tambayoyin da ake shirin fitarwa ga ɗalibai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Select an episode
0:00 0:00