About this episode
2026-03-14BBC HausaShirin Safe (2:00am EST)* Shugaba Trump ya ce Amurka ta kai hare-hare a kan abin da ta kira wurare na soja a tsibirin Kharg, babbar tashar fitar da man Iran a tekun Fasha. (Labari mai alaƙa: DWHausa Safe #6)* Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla ma’aikatan lafiya goma sha biyu (12) aka kashe a wani hari da Isra’ila ta kai kan wani a ƙaramin asibiti a kudancin ƙasar.* Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, ta gargaɗi ƴan ƙasar musamman a jihohin Arewa game da yiwuwar ɓarkewar cutar sanƙarau yayin da aka fara shiga yanayin tsananin zafi.* Ƙwayar cutar da ta fi sa sankarau din annoba shine ake samu mafi yawan ci a kusan arewacin Najeriya. In haka ya faru, sai mu yi ta bawa mutane ƙanana-ƙananan shawara na kar su [???]. Ba wani cunkoso, a dinga buɗe windo, sannan mu dinka sa mutane suna ɗan wanke baki da drip.* (A filin Gane Mini Hanya) Har wa yau a Najeriya, majalisar dattawan ƙasar ta ce za ta sake gayyatar shugabancin kamfanin mai na ƙasar: NNPC, kan yadda wasu maƙudan kuɗaɗe suka yi ɓatan dabu a tsakanin shekarar ta 2017 zuwa 2023.* Yaya ma za a yi a ce tiriliyan ɗari biyu da goma (210T) sun ɓace ko an rasa su, ba a bamu ƙididdiga da ta gamsar da mu ba? A ina kuka kashe su? A me kuka kashe?* Mai gabatarwa: BBC Hausa Muhammad Annur MuhammadDW HausaShirin Safe (2:30am EST)* Mai gabatarwa: DW Hausa Mohammed Tijjani Hassan* (A shirin Sharhunan Bayan Labarai) A Najeriya, wata cibiyar samar da zaman lafiya ta horas da masu bukata ta musamman kan matakai da hanyoyin da za su bi domin kare kansu a yanayin rashin tsaro da kuma faɗace-faɗace.* Yayin da a gefe guda, kungiyoyin kare muhalli suka fara gangamin wayar da kan al’umma domin dakile ambaliyar wato ambaliyar ruwa a arewacin Nijeriya.* A Nijar kuwa sabuwar taƙaddama ce ta kunno kai a tsakanin gwamnati da shugabannin ƙasashen Turai kan buƙatar da suka sake miƙawa ta sakin hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum wanda ake tsare da shi yau kusan shekaru biyu.* A Ghana kuwa za a ji ƙarin bayani kan wani tsari da aka samar wanda ya tanadi kare yara daga hatsarin da ke tattare da haƙar ma’adinai ta bayan fage wato Galamsey.* Trump ya ce Iran ta faɗi a yaƙi kuma a yanzu haka tana son a cimma yarjejeniya. (Labari mai alaƙa: BBCHausa Safe #1)* An kai hari kan ofishin jakadancin Amurka da ke Iraqi a wannan safiya ta Asabar.* Wani gagarumin harin Rasha ya yi ajalin mutane biyu a yankin Kiev na Ukraine.2026-03-13RFI HausaLabaran RFI Hausa na ƙarfe 5 na yamma agogon Najeriya da Nijar 13-03-2026… • RFI Hausa* Mai gabatarwa: RFI Hausa Shamsiyya Haruna* An ji ƙarar fashewar abubuwa masu yawa a tsakiyar birnin Tehran dai dai lokacin da ake ci gaba da ƙidayar waɗanda suka mut