Yara sama da miliyan 6 ne ke fama da tamowa a Arewacin Najeriya - ICRC
HomeBakonmu a Yau › Episode

Yara sama da miliyan 6 ne ke fama da tamowa a Arewacin Najeriya - ICRC

3:38 Mar 11, 2026
About this episode
Ƙungiyar agaji ta ICRC ta ce aƙalla yara ƙanana da ke ƙasa da shekaru 5 miliyan 6 da dubu 400 ke fama da tamowa a yankunan arewa maso gabashin Najeriya da ya kwashe shekaru 15 ya na fama da rikice rikicen Boko Haram da arewa maso yamma da ke fama da rikicin ƴan bindiga, sai kuma arewa ta tsakiya da ke fama da rikicin manoma da makiyaya. Mai magana da yawun ƙungiyar Usman Kundili Bukar ya bayyana haka a tattaunarsa da Bashir Ibrahim Idris. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu.......
Select an episode
0:00 0:00