Ɗaruruwan ƴan Najeriya sun yi zanga-zanga akan gyaran dokar zaɓe
HomeBakonmu a Yau › Episode

Ɗaruruwan ƴan Najeriya sun yi zanga-zanga akan gyaran dokar zaɓe

3:24 Feb 10, 2026
About this episode
Ɗaruruwan ‘yan Najeriya a jiya Litinin, sun gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Abuja, domin bayyana ɓacin ransu dangane da jan ƙafa a kan gyaran dokar zaɓe da majalisar ƙasar ke yi, musamman kan matakinta na ƙin amincewa da batun tilasta wa hukumar zaɓe sakin sakamako kai-tsaye daga rumfuna a shafinta na yanar gizo.Kan wannan   Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Ibrahim Bello Rigachikun, tsohon ɗan Majalisar Tarayya, kuma ƙwararren lauya a Najeriyar. Latsa alamar sauti domin sauraron tattaunawar
Select an episode
0:00 0:00